Kashi 62 cikin 100 na masana tattalin arzikin sun bayyana cewa, cece kucen da ake samu game da shirya zaben shugaban kasar Amurka yana neman yin tasiri game da makomar tattalin arzikin kasar, yayin da kaso 35 cikin 100 na masanan ke ganin cewa, zaben na watan Nuwambar bana wata dama ce da za ta iya daga likafar tattalin arzikin Amurkan.
A cewar sashen kula da al'amurran ciniki na Amurka, tattalin arzikin kasar da ake sa ran karuwarsa da kashi 1.2 a watanni 8 na farkon wannan shekara, sakamakon dambarwar siyasar kasar ya karu ne da digo 8 a watanni ukun farko na wannn shekara.
Alkaluman sun nuna cewa da wuya tattalin arzikin Amurkar ya karu da kashi 2 a watannin hudun karshe na wannan shekara. (Ahmad Fagam)