in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata mata daya ta mutu a sakamakon harin bindiga da aka kai a birnin Austin na kasar Amurka
2016-08-01 10:56:19 cri
A jiya ne wata mace ta rasa ranta yayin da mutane da dama suka ji rauni,sakamakon wani harbin bindiga da aka kai a birnin Austin dake jihar Texas ta kasar Amurka.

'Yan sandan birnin Austin sun wallafa a shafinsu na internet a jiya Lahadi cewa, an kai hari da bindiga a tsakiyar birnin a wannan rana da karfe 3 na safe, inda suka gargadi jama'a da kada su je tsakiyar birnin. Daga bisani bayan mituna talati, sai 'yan sandan suka sake sabunta bayanan da suka bayar cewa, al'amura sun dai-dai a wurin da aka kai harin.

Kafofin watsa labaru na wurin sun bayar da rahoton cewa, an kashe wata mace a sakamakon harin, yayin da mutane da dama suka ji rauni. Har yanzu dai ba a san asalin maharin da kuma dalilinsa na kai harin ba.

A ranar 7 ga watan Yuli ma, an taba kaiwa 'yan sanda a birnin Dallas dake jihar Texas rin wannan hari, wanda ya haddasa mutuwar 'yan sanda 5, yayin da wasu'yan sanda 7 suka ji rauni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China