in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmai 14500 na kasar Sin za su je Saudiyya domin gudanar da aikin hajin shekarar bana
2016-08-20 13:06:30 cri

Bisa labarin da hukumar kula da harkokin addini ta kasar Sin ta bayar, an ce, musulmai 14500 na kasar Sin za su isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin haji a wannan shekara. Daga cikinsu, akwai musulmai daga lardunan Henan, Hebei da yankin Mongolia ta gida, kuma sun tashi daga filin jiragen saman birnin Beijing a yau ranar 20 ga wata.

Mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin addini ta kasar Sin Zhang Yan ya bayyana a filin jiragen saman cewa, jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar na dora muhimmanci sosai ga aikin haji, kuma hukumarsa tana bin manufofin bin addini cikin 'yanci, da yin hadin gwiwa tare da hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da ayyukan kiwon lafiya, da tabbatar da tsaro, ba da jagoranci, samar da jiragen saman musamman, samar da abinci da wurin kwana, da yin jigila da dai sauransu don samar da sauki ga musulman da suke aikin haji. Hakazalika kuma, Mr Zhang yana fatan musulman za su dauki matakan tinkarar zafin yanayi da tabbatar da tsaronsu don shaida mutuncin kasar Sin da na musulman kasar yadda ya kamata.

An ce, ya zuwa ranar 19 ga wata, musulmai 11000 na kasar Sin sun tashi zuwa kasar Saudiyya ta jiragen saman musamman guda 37. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China