in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mahajjatan da suka mutu a turmutsatsu ya zarta 700
2015-09-24 20:52:07 cri
Hukumomin kasar Saudi Arebiya sun ce ya zuwa yanzu, mahajjatan da suka mutu a sakamakon turmutsutsu yayin gudanar da aikin hajji a birnin makka a yau alhamis ya karu zuwa mutane 717, yayin da adadin wadanda suka samu raunuka ya kai 805.

Hukumar tsaro da kare rayukan jama'a ta Saudi Arebiya ne ta sanar da karuwar adadin a shafin ta na twitter.

Wadanda iftila'in ya rutsa da su, sun fito ne daga kasashen duniya dabam dabam.

Lamarin dai ya afku ne a daidai lokacin da mahajjatan ke ta tururuwar jifar shaidan, wanda daya ne daga cikin rukunonin aikin hajjin.(Ahmed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China