Kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya bayyana ma manema labarai a nan birnin Beijing, yace Sin tana mika ta'aziyar ta tare da juyayi ga iyalan wadanda suka rasu ko suka jikkata.
Mahukuntar kasar Saudiya sun tabbatar da cewar akalla mutane 717 ne suka rasu. Wannan ne karo na biyu da irin haka ya faru cikin wata daya. A farkon watan maniyyata 111 suka rasu sanadiyar faduwar karfen daukan kaya wanda ya fado daga ginin masallacin Harami da ake fadadawa a birnin Makka.(Fatimah)