A sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar IS suka kai kasar Saudiyya a farkon wannan shekara da kuma karfen daukan kaya da ya fado kan masu Ibada a babban masallacin harami da ke birnin Makka a kwanan baya wanda ya halaka mutane sama da 100, gwamnatin kasar ta Saudiyya tana sanya matukar muhimmanci a kan matakan tsaro a lokacin aikin hajji na wannan shekara, inda aka girke ma'aikatan tsaro kimanin dubu 100 da ma'aikatan kashe gobara sama da 3000 da kuma motocin kashe gobar kusan 500 a wuraren da ake aikin hajji.
Ban da haka, domin magance matsalar cutar MERS, ma'aikatan jiyya kusan dubu 30 a asibitoci daban daban da ke birnin Makka su na cikin shirin ko ta kwana don tinkarar duk wasu abubuwa za su iya kunno.(Lubabatu)