Ministan kwadago da samar da aikin yi na Najeriya Chris Bgige ne ya yi wannan gargadi a Abuja, babban birnin kasar, a lokacin bikin kaddamar da manufofin kasar game da kaurar ma'aikata wanda kungiyar kula da kaurar jama'a ta kasa da kasa(IOM) da kungiyar kwadago da duniya(ILO) suka tsara.
Minista Ngige, ya bayyana cewa, wasu jaridun cikin gida da na kasashen duniya sun wallafa wasu rahotanni game da 'yan Najeriyar da suka rasa rayukansu a kokarin shiga kasashen Turai ta tekun Bahar Rum da Hamadar Sahara.
Ya ce, gwamnatin Najeriya tana dora muhimmanci sosai kan dokokin da suka shafi kwadago, kasancewarta kasa mai asali da kyakkyawar makoma, haka kuma tana amfana da gudummawar da ma'aikatan suke bayarwa.
Ngige ya ce, an inganta wannan doka ce, saboda hadarin da ke tattare da kaurar da jama'a suke yi ba bisa ka'ida ba da kuma tasirin hakan ga albarkatun kasa da kuma ci gabanta.
Tun da farko a nasa jawabin, babban jami'in kungiyar kula da kaurar jama'a ta kasa da kasa(IOM) ya ce, akwai bukatar daukar muhimman matakan aiwatar da wadannan manufofi, ta yadda haka za ta cimma ruwa.(Ibrahim)