Ministan wanda ya bayyana hakan lokacin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na kungiyar marubuta labaran harkar makamashi ta kasa da ya gudana a birnin Legas, ya ce, daga watan Janairu zuwa yanzu, an samu rahotannin fasa bututan mai 1,600, adadin da ke nuna cewa, daga shekarar 2010 zuwa 2015, an samu rahotannin fasa bututan mai sama da 3,000.
Kachikuwu ya ce, faduwar farashin mai a kasuwannin duniya da kuma yadda ake kai hare-hare kan bututan man fetur da na iskar gas a yankin, sun yi mummunan tasiri kan kudaden shiga da kasar ta ke samu, lamarin da ya sanya gwamnati rashin kudaden da za ta iya aiwatar da kasafin kudin shekarar 2016.
A saboda haka, ministan ya yi kira da a dauki matakan da suka wajaba, don magance wannan matsala. Yana mai cewa, lokaci ya yi da Najeriyar za ta yi karatun ta nutsu, ganin cewa babu tabbas game da farfadowar farashin man kamar yadda ake ta rade-rade.
A 'yan watannin da suka gabata ne dai kungiyar tsagerun 'yankin Niger Delta ta NDA suka tarwatsa wasu na'urorin mai mallakar kamfanonin mai na kasashen waje da ke aikin hako mai a yankin.(Ibrahim)