in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya kaddamar da yakin neman babban zaben kasar da ke tafe
2016-08-15 11:32:16 cri

A jiya ne shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kaddamar da yakin neman babban zaben kasar na shekarar 2016 a hukunce a birnin Cape Coast, inda magoya bayansa kimanin dubu 16 suka halarci bikin.

A jawabin da ya gabatar John Dramani Mahama ya bayyana cewa, a cikin shekaru 3 da suka gabata, a karkashin jagorancin jam'iyyar NDC, gwamnatin kasar ta cimma manyan nasarori a fannonin daidaita tattalin arziki, da warware matsalar makamashi, da kuma raya muhimman ababen more rayuwa.

Ya kuma yi alkawari cewa, idan ya ci gaba da rike mukaminsa na shugaban kasar, zai yi kokarin rage hauhawar farashin kayayyaki, kana da tabbatar da karuwar GDPn kasar cikin sauri. Ana sa ran tattalin arzikin kasar Ghana zai kara samun kyautatuwa a shekarar 2017, bayan da asusun IMF ya taimaka wa kasar .

Rahotanni na cewa, a cikin makoni biyu masu zuwa, jam'iyyar NDC a kasar Ghana za ta fitar da sanarwa game da manufofi da kuma shirye-shiryenta.

Kamar yadda aka shirya, za a gudanar da babban zaben kasar Ghana na shekarar 2016 a ranar 7 ga watan Disamba. Dan takarar jam'iyyar NPP Nana Dankwa Akufo-Addo shi ne zai fafata da John Dramani Mahama a zaben shugabacin kasar, ko da yake har yanzu bai fara nasa yakin neman zaben ba tukuna.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China