in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya bukaci a bunkasa masana'antu don ci gaban kasashen Afrika
2016-07-22 10:45:01 cri

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya ce, muddin ana bukatar ci gaba mai dorewa a kasashen Afrika, ya zama tilas a samar da hanyoyin ci gaban masana'antu.

Mahama ya furta hakan ne cikin jawabinsa na bude taron koli na kasashen yammacin Afrika game da masana'antu, inda ya jaddada cewar, wannan mataki zai taimaka wajen rage barazana ga karfin tattalin arzikin yankunan, tare kuma da samar da ayyukan yi ga al'umma.

Kungiyar raya ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma wato ECOWAS ce ta shirya taron, da nufin samar da sahihin tsari don habaka ci gaban masana'antu a nahiyar.

Taron na wuni guda mai taken: "bunkasa zuba jari don habaka masana'antun ECOWAS" ya mai da hankali ne wajen tattauna batutuwan da suka shafi bunkasuwar masana'antu da ci gaban kamfanoni masu zaman kansu a yammacin Afrika.

Ya ce, kasashen yammacin Afrika suna bukatar dabarun da za su taimaka wajen ci gaban muhimman bangarori da suka hada da samar da lantarki don ci gaban masana'antu, da magance yunwa da rashin abinci mai gina jiki, da inganta rayuwar mazauna karkara, da dogaro da kai ta fuskar samar da abinci, da kuma samar da muhimman ababan more rayuwa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China