in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Ghana ta ce a shirye take ta samar da tsaro a lokacin zaben kasar
2016-06-29 12:08:44 cri

Shugaban rundunar sojin kasar Ghana Marshall Samson Oje, ya fada a jiya Talata cewar, dakarun kasar za su dauki dukkan matakan da suka dace domin samar da zaman lafiya a lokacin babban zaben kasar wanda ke tafe a nan gaba.

Da yake zantawa da manema labaru a birnin Accra a jiya Talata, Oje, ya fada cewar, ko da yake al'amurra sun fara daukar zafi tun kafin gudanar da zaben kasar, amma ya tabbatar da cewar, za'a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ya ce, rundunar sojin kasar za ta hada kai da 'yan sanda domin tabbatar da doka da oda a lokacin zaben da bayan zaben na bana, sannan ya bukaci kafafen yada labaran kasar da su gudanar da aikinsu bisa kwarewar ta hanyar ba da dama ga kowane bangare ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba.

Shugaban kungiyar 'yan jaridun Ghana Affail Monney, ya gargadi kafafen yada labarun kasar da su guji aikata duk wani abu da ke iya jefa kasar cikin rudani a lokacin zaben kasar.

Kasar ta yammacin Afrika ta kasance zakaran gwajin dafi wajen tabbatar da demokaradiyya da zaman lafiya, kuma ana sa ran kasar za ta nunawa duniya halin dattaku ta hanyar gudanar da zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokokin kasar 275 a watan Nuwamba cikin kwanciyar hankali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China