Rahotanni daga Ghana na cewa, an kara gano gawawwakin wasu mutanen da suka mutu a hadarin kwale-kwalen da ya nutse ranar Lahadi a kogin Volta da ke kusa da garin Yeji a kudancin kasar.
Tawagar masu aikin ceto ta bayyana cewa, ta gano gawawwakin yara kanana guda 6 'yan kasa da shekaru 3. Sai dai wasu da suka tsallake rijiya da baya, sun bayyana cewa, mai yiwuwa wasu mutane da dama sun nitse.
Da yake yiwa manema labarai karin haske game da yawan mutanen da suka mutu sanadiyar hadarin, wani jami'in yankin ya bayyana cewa, kwale-kwalen yana dauke da mutane ne fiye da kima.
Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin zakulo wadanda ke da sauran nunfashi.
Alkaluma na nuna cewa, yawan wadanda suka riga mu gidan gaskiya ya karu zuwa 8.(Ibrahim)