in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Ghana ta musanta zargin cin hanci da ake yiwa shugaba Mahama
2016-06-16 11:59:38 cri

Gwamantin kasar Ghana ya yi watsi da zargin da ake yiwa shugaban kasar John Dramani Maham na karbar kyautar mota daga wani kamfanin gine gine na kasar Burkina Faso.

A sanarwar da ministan sadarwa na kasar Dr. Edward Omane Boamah ya fitar, ya tabbatar da cewa, motar an ba da kyautar ta ne domin amfanin gwamnati ba na kashin kai ba.

A jiya Laraba cikin wani shirin gidan radiyo da aka watsa a kasar, aka ambato wani kamfanin gine gine na Kanazoe Freres na kasar Burkina Faso, ya bai wa shugaban kasar Ghana kyautar mota a shekarar 2012.

A shekarar 2011 ne dai gwamnatin kasar Ghanan ta baiwa kamfanin gine ginen kwangilar ginin katangar ofishin jakadancin Ghana dake Burkina Faso mai tazarar mita 673 bayan da kamfanin ya yi nasara a yayin tallata kwangiyar aikin gina hanya, wadda kungiyar tarayyar Turai ta dauki nauyin gudanar da shi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China