Boren da kungiyoyi ke yi a garin Badun, babban birnin jihar Oyo, ya gurgunta al'amura a birnin a jiya Litinin, lokacin da daliban makarantar sakandare suka fara barnata kayayyakin jama'a, ciki har da gidan gwamnan jihar Abiola Ajimobi,domin nuna bacin ransu kan shirin gwamnatin jihar na cefanar da sashen ilmi.(The Guardian)
A gobe Talata ne hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, za ta gurfanar da Azibaola Robert, dan uwan tsohon shugaba Goodluck Jonathan, bisa zargin da ake masa na karbar kwangilar dala miliyan 40 daga tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki.
Wannan mataki na zuwa ne kwana guda bayan da tsohon shugaban kasar ta Najeriya ya amince cewa, gwamnatin shugaba Buhari tana bincikarsa bisa zargin cin hanci da rashawa, zargin da tsohon shugaban ya musanta.(The Punch)