in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Quadri Aruna, "Bakin doki" na Najeriya na kokarin cimma burinsa a wasan kwallon tebur
2016-08-11 13:57:51 cri

Ranar Talata 9 ga watan nan ne ranar haihuwar Quardri Aruna, dan wasan kwallon tebur ajin maza a gasar Olympics dake gudana yanzu haka a birnin Rio na kasar Brazil, a kuma wannan rana ne dan wasan dan Najeriya ya cimma nasarar shiga zagaye na biyu na gasar kwallon tebur.

A matsayin sa na wani babban "Bakin doki" a gasar wasannin kwallon tebur ta wasannin Olympics, duk da yake bai lashe zakaran wasa Ma Long dan wasan kasar Sin ba a wasan da suka tashi 0:4, duk da hakan ya samu matukar yabo.

Aruna ya kasance dan wasa na farko a nahiyar Afirka, wanda ya shiga zagaye na biyu a wasannin na Olympic a tarihi, hakan ya sanya shi samun goyon baya sosai a gasar ta Rio.

A yayin da yake fuskantar abokin karawar sa Ma Long, wanda ya fi shi kwarewa sosai, Aruna ya yi iyakacin kokarinsa a gasar, ko da yake bai cimma nasara ba, amma ya ce ya kece raini sosai a duk lokacin gasar.

"ba na jin tsoron karawa da Ma Long, saboda ban damu da lashe gasar ba, na yi wasa kamar yadda na yi lokacin karawa ta da Chuan Chih-Yuan, da Timo Boll, ban ji wani matsi ba, kuma na kece raini a wasan. A ganina na cimma buri na na karawa da Ma Long, saboda Ma Long dan wasan kwallon tebur ne da na fi so, na kan nemo bidiyon wasan sa na kalla."

Tun lokacin yarantakarsa, Aruna ya soma wasan kwallon tebur. A mahaifar sa dake birnin Oyo, cikin sauki ya rika samun tebur don gudanar da wasan kwallon tebur, sakamakon ayyukan da iyayensa suke yi. Kuma tun daga lokacin ne, Aruna ya soma sha'awar wannan wasa.

"Na soma wasan kwallon tebur tun ina dan shekaru kusan 7, a lokacin na kan yi nishadi ne kawai idan ina buga wasan. Ban taba tunanin wata moriya da kwallon tebur za ta kawo min ba. A wancan lokaci, ina wasan kwallon tebur a kusan ko wace rana, saboda gaskiya ina son wasan kwarai."

An haifi Aruna a shekarar 1988, ya kuma taba shiga gasa zagaye na biyu ta kofin duniya, ta wasan kallon tebur da ta gudana a Jamus a shekarar 2014, hakan ya sanya matsayinsa a duniya ya karu zuwa 30, ta yadda hukumar kwallon tebur ta duniya ta ba shi lambar yabo, ta dan wasa da ya fi nagarta a waccan shekara. Aruna yana fatan zai iya ci gaba da wasa a wasannin Olympics masu zuwa, kamar yadda Segun Toriola ya yi, a lokacin yana dan shekara 32 da haihuwa.

"zan ci gaba da wasan kwallon tebur, har zuwa lokacin da na gajiya. Ba zan yi watsi da wasan cikin sauki ba. Zan yi iyakacin kokari cikin wannan wasa, har zuwa lokacin da yanayin jiki zai hana ni buga wasan."

Game da Aruna, shugaban kungiyar 'yan wasan kwallon ta kasar Sin Ma Long, shi ma ya jinjinawa masa. Ya ce,

"A matsayinsa na dan wasan kwallon tebur daga kasashen Afirka, ba abu ne mai sauki ya samu shiga zagaye na biyu na gasar ba, kuma kafin hakan ma ya cimma nasara lashe wasan sa da Chuan Chih-Yuan, da Timo Boll, wanda hakan duk ya nuna cewa, yana da halin musamman a wasan kwallon tebur. Yana kuma da kwarewa wajen sarrafa hannu, da yadda yake juya kafafu, da kuma buga kwallo daga nisa da tebur.

A ganin Ma Long, a matsayin wani dan wasan motsa jiki daga nahiyar Afirka, Aruna ya shiga gasar wasannin Olympics, har ma ya shiga wasannin fid da mafi nagarta hudu, hakan na da amfani sosai wajen yaduwar wasan kwallo tebur, ya kuma bayyana ma'anar alamar zobba guda 5.

"wannan abu ya yi kyau, ta haka ne ake iya samun yaduwar wasan kwallon tebur a Afirka, wannan shi ne wasannin Olympics, zobba guda 5 na hade da manyan bangarorin duniya guda biyar."

A nasa bangaren, Aruna shi ma ya bayyana cewa, za a samu 'yan wasa da yawa, da za su iya shiga gasar kwallon tebur ta wasannin Olympics daga nahiyar Afirka a nan gaba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China