Dan wasan kasar Kaya Adwoa Forson, mai shekaru 14, ya kasance dan kasar Ghana na farko da ya shiga gasar ninkaya a wasannin a katafaren filin ninkaya na Rio a ranar 8 ga watan Augusta.
Vanderpuye ya ce yana matukar alfahari kasancewar kasar Ghana tana daga cikin wadanda ke halartar wasannin na kasa da kasa, ya bayyana kyakkyawar fata ga tawagar 'yan wasan kasar da cewar, za su samu babbar nasara a gasar wasannin na Rio.
A sakon da ya gabatar a madadin shugaban kasar John Dramani Mahama, Vanderpuye ya bayyana cewar, ya kamata tawagar 'yan wasan su tuna cewar suna wakiltar al'ummar kasar Ghana ne baki daya, kuma jama'ar kasar gaba daya sun zuba musu ido.
Sannan ya bukace su da su tsaya tsayin daka domin ganin hakarsu ta cimma ruwa, kuma su nuna kyawawan halayansu.
Tawagar 'yan wasan na Ghana ta kunshi 'yan wasannin 16 wadanda suka halarci gasar wasannin na Olympic a karon farko, inda za su shiga wasannin nau'i 5 a gasar wasannin ta Rio.(Ahmad Fagam)