in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Quadri Aruna ya kafa tarihi a gasar wasannin Olympics ta Rio
2016-08-09 11:34:15 cri


Yayin da Quadri Aruna ya lashe lambar yabo ta dan wasan kwallon tebur mafi kwarewa a shekarar 2014, wanda hukumar wasan kwallon tebur ta duniya ta bayar, jama'a sun nuna shakku ga wannan dan wasan daga tarayyar Najeriya, wanda a lokacin ya samu wannan lambar yabo maimakon dan wasan kasar Sin.

A gasar wasannin Olympics ta Rio ta wannan karo, Aruna ya doke Chuan Chih-Yuan daga yankin Taiwan na kasar Sin, da kuma Timo Boll daga kasar Jamus, inda ya shiga cikin jerin 'yan wasa takwas da za su shiga gasar a zagaye na uku. Hakan dai ya ba shi damar kafa tarihin zama dan wasa daga nahiyar Afirka, da zai shiga zagaye na uku a wasan a gasar wasannin Olympics. Yanzu dai za a ga daya daga 'yan wasan nahiyar Afirka cikin masu buga wasan kwallon tebur a manyan gasannin duniya.

Wannan ne karo na biyu da Quadri Aruna daga tarayyar Najeriya, ya halarci gasar wasannin Olympics. A gun gasar wasannin Olympics ta birnin London da aka gudanar a shekaru hudu da suka wuce, ya gaza samun damar shiga zagaye na biyu a gasar. A wancan lokacin, bai jawo hankalin jama'a sosai ba. Aruna ya fara jawo hankalin masu sha'awar wasan kwallon tebur na kasar Sin ne, tun daga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur ta shekarar 2014, a wasan zagaye na uku, inda ya gamu da mashahurin dan wasan kasar Sin Zhang Jike. Aruna ya samu nasara a sashen wasa na farko da ci 11 da 6, koda yake bai cimma nasara a karshe ba, amma ya shaida karfin kwarewar sa, a matsayin sa na dan wasa daga nahiyar Afirka, kana Zhang Jike ya nuna yabo gare shi.

A lokacin, Zhang Jike ya bayyana cewa, wasan da ya fuskanci kalubale a wannan karo shi ne wasan da ya buga tare da Aruna, babu shakka kwarewar sa ta kai matsayi na 32 a duniya. Akwai yiwuwar wani dan wasa ya samu nasara a sashen wasa daya kawai, amma ya doke 'yan wasa uku a wannan karo, hakan ya shaida matukar kwarewarsa.

Kowa ya sani cewa, 'yan wasa daga nahiyar Asiya da Turai sun fi samun kwarewa a wasan kwallon tebur a duniya, amma Aruna ya kawo imani ga nahiyar Afirka a wannan fanni. Bayan da ya doke Boll a wannan karo, Aruna ya bayyana cewa, yanzu ya ji farin ciki sosai, ya cimma burinsa, bai taba tunanin zai kai ga shiga zagaye na uku a gasar wasannin Olympics ba, amma ya yi imani sosai da ci gaba da yin gasa.

Ban da dan wasan kwallon tebur, Aruna ya gudanar da aiki a sojojin kiyaye tsaro na kasar Nijeriya. Ya ce, wannan aiki ya zama hanya ta gaba bayan da ya janye daga dandalin wasan kwallon tebur.

Ga Aruna, shiga zagaye na uku ya kasance kyauta ta tunawa da zagayowar ranar haihuwarsa da ya samu, kafin ranar haihuwarsa ta zo. A ranar 9 ga wannan wata ne dan wasan zai cika shekaru 28, zai kuma buga wasa tare da dan wasan kasar Sin Ma Long, wanda ke matsayin farko a duniya. Kafin wannan karo, 'yan wasan su biyu ba su taba buga gasa tare ba, don haka ake bagen ganin irin rawar da Aruna zai taka a wannan wasa.

Aruna dan wasan nahiyar Afirka ya samu sabon matsayi na duniya a wasan kwallon tebur, kana ya shiga zagaye na uku a gasar wasannin Olympics ta Rio, yana kuma kokarin cimma burinsa da samun ci gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China