in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan 'yan gudun hijira, tawaga musamman ce mai halartar gasar wasannin Olympics ta Rio
2016-08-08 13:10:30 cri

Ko da yake an samu yake-yake a kasashensu, kuma sun rasa gidajensu, amma a karkashin tutar Olympics, 'yan gudun hijira daga kasashen duniya da dama, da yankuna daban daban suna kokarin nuna kwarewarsu a wasanni.

Wannan ce tawagar wakilan 'yan gudun hijira a gasar wasannin Olympics ta Rio a wannan karo. Wannan ne karo na farko da aka kafa tawagar wakilan 'yan gudun hijira don halartar gasar wasannin Olympics, kana shi ne babban aiki da kwamitin wasannin Olympics na duniya ya gudanar don taimakawa 'yan wasa dake gudun hijira wajen ci gaba da shiga wasannin motsa jiki.

Shugabar tawagar wakilan 'yan gudun hijira Tegla Loroupe ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a kwanan baya cewa, wannan tawaga na fuskantar kalubale da dama, za ta kuma taimakawa mutane su kara saninsu kan mummunar matsalar 'yan gudun hijira, za su gano 'yan gudun hijira duk daya suke da sauran mutanen duniya. Ko da yake sun rasa gidajensu, amma suna da hakki iri daya da dukkan mutanen kasa da kasa da yankuna a duniya.

Wannan tawaga tana kunshe 'yan wasa 10, ciki har da biyar daga kasar Sudan ta Kudu, biyu daga kasar Syria, biyu daga Congo Kinshasa, da kuma daya daga kasar Habasha, wadanda za su halarci gasar guje-guje da tsalle-tsalle, iyo, wasan judo da sauransu.

Kwamitin wasannin Olympics ta duniya wato IOC ya zabi wakilan 'yan gudun hijira, da tabbatar da asalinsu da yanayinsu da kuma karfinsu a fannin wasanni da dai sauransu.

Shugaban kwamitin IOC Thomas Bach ya sanar a gun babban taron MDD karo na 70 da aka gudanar a shekarar 2015 cewa, kwamitin IOC ya yi maraba da 'yan wasa masu kwarewa 'yan gudun hijira, wadanda ba su iya wakiltar kasashensu da su halarci gasar wasannin Olympics ba.

A watan Maris na bana, kwamitin IOC ya gabatar da wata sanarwa, inda ya sanar da za a kafa tawagar wakilan 'yan gudun hijira wadda za ta halarci gasar wasannin Olympics ta Rio. An kafa tawagar ne a ranar 3 ga watan Yuni, ban da 'yan wasa, kwamitin IOC ya kuma zabi masu horaswa da jami'ai na wannan tawaga.

A shekarun baya-baya nan, ana samun yake-yake da talauci a yankin gabas ta tsakiya da kuma nahiyar Afirka, don haka 'yan gudun hijira daga wadannan yankuna sun tsere daga kasashensu zuwa nahiyar Turai, matakin da ya haddasa matsalar 'yan gudun hijira. Bach ya bayyana cewa, an kafa wannan tawagar wakilan 'yan gudun hijira ce, don yada sakon nuna kyakkyawan fata ga dukkan 'yan gudun hijira a duk fadin duniya, da sa dukkan duniya ta gano matsalar 'yan gudun hijira, da nuna wa duniya cewa, 'yan gudun hijira daya suke da sauran al'ummar duniya.

Watakila wadannan 'yan wasan tawagar 'yan gudun hijira ba za su samu kwarewa bisa sauran mashahuran 'yan wasan duniya ba, amma kwamitin IOC ya tabbatar da wadannan 'yan wasa 10, cewa za su halarci gasar wasannin Olympics ta Rio bayan da aka yi la'akari daga dukkan fannoni. Ko da yake abu ne mai wuya su samu lambobin yabo, amma shigarsu cikin gasar na da babbar ma'ana, domin dai sun samu halartar gasar wasannin na Olympics.

Wadannan 'yan wasa ba su wakilci ko wace kasa ko yanki ba, amma ana gudanar da bikin maraba da zuwansu a kauyen wasannin Olympics. Kana a gun bikin bude gasar wasannin Olympics ta Rio, za kuma su fita kafin tawagar kasar Brazil mai daukar bakuncin gasar.

Idan sun samu lambobin yabo a wasannin na wannan karo, za a daga tutar kwamitin IOC, da yin taken kwamitin IOC. Lambobin yabo da suka samu ba su da nasaba da kasashensu ko yankunansu, ko da yake kasashensu su ma sun tura tawagarsu don halartar gasar wasannin Olympics ta Rio.

Ko da yake ba su iya wakilcin kasashensu da yankunansu a gasar ba, wadannan 'yan wasa wakilan 'yan gudun hijira suna bakin ciki game da hakan, a hannu guda sun zama abun alfahari, kuma wakilan dukkan 'yan gudun hijira na duniya bisa halartar su gasar ta wasannin Olympics. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China