Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, fadar mulkin kasar cewa, wannan batu da jaridar ta wallafa babu kamshin gaskiya a cikinsa.
Ya ce, shugaba muhammadu Buhari yana daukar dukkan 'yan Najeriya daya ba tare da nuna wani bambancin addini, kabila ko yankunan da suka fito ba. Kuma gwamnatinsa ta gaji rikicin Boko Haram ne wadda ke fatan raba kan 'yan kasar ta hanyar amfani da addini. A saboda haka, gwamnatinsa ta ba da muhimmanci wajen yakar mayakan na Boko Haram.
Bugu da kari, Malam Garba Shehu ya karyata sharhin da jaridar ta wallafa a ranar 30 ga watan Yyulin, wanda ke cewa, yunwa tana halaka yara a yankin arewacin kasar.
A cewarsa, gwamnatin Najeriya ba ta da ikon karkata kudaden agajin da aka tanadarwa 'yan gudun hijira da ke tsugune a sansanonin da aka tanada bisa kowa ne irin dalili.(Ibrahim)