in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kafofin watsa labaru na Afrika sun goyi bayan matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun tekun kudancin Sin
2016-07-12 13:41:32 cri

A kwanan baya, kafofin watsa labaru na wasu kasashen Afrika sun ba da bayanai domin nuna goyon bayansu ga matsayin da kasar Sin ta dauka kan batun tekun kudancin Sin, tare da bayyana hakikanin burin da kasar Amurka take da shi game da hukuncin da za a yanke kan batun tekun kudancin Sin.

Wasu muhimman jaridun kasar Afrika ta kudu sun bayar da bayanai cewa, kasar Amurka ta hana bunkasuwar kasar Sin ta hanyar kitsa shirin yanke hukunci kan batun tekun kudancin Sin. A cikin bayanai, an bayyana cewa, kasar Amurka tana daukar kasar Sin a matsayin kasar da ke kawo mata kalubale a fannin neman mallakar duniya.

Jaridar Herald, jarida mafi girma a kasar Zimbabwe ta wallafa wani sharhi cewa, kasar ta goyi bayan matsayin da kasar Sin ke dauka kan batun tekun kudancin Sin. Inda ta kara da cewa, kasar Sin ta nace ga daidaita batun kasa da teku ta hanyar yin shawarwai cikin ruwan sanyi bisa tarihi da klma dokokin kasa da kasa, kana kasar Sin ba za ta yarda wasu kasashe su tsoma baki kan batun ba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China