in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jaddada muhimmancin mai da hankali kan tsaron jama'a wajen yaki da ambaliyar ruwa
2016-07-21 10:50:05 cri
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya yi kira da a kara rubanya kokari domin sanya ido da kuma yaki da ambaliyar ruwa a cikin kasar, tare da jaddada muhimmancin mai da hankali kan tsaron al'umma. Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake yi a kasar Sin tun cikin watan Yuni sun janyo asara sosai kuma za a ci gaba samun ruwan sama masu karfi a kuma wasu yankuna. A yayin wata ziyarar gani da ido a yankin jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui dake arewa maso yammacin Sin, mista Xi ya bayyana cewa a yayin wani zaman taron cewa kwamitocin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatocin yankuna a matakai daban daban za su karfafa ikonsu da fada a jinsu wajen sanya ido kan ambaliyar ruwa da kuma ayyukan ceto.

Wadanda suka kaucewa ayyukansu, kuma suka janyo asarar mutane da dukiyoyi masu yawa za su dauki alhaki bisa wuyansu, a cewar kashedin shugaba Xi Jinping.

Haka kuma ya jaddada kan wani sanya ido sosai na sauye sauyen yanayi da kuma ruwan sama, da yin nazari mai kyau kan matsalar ambaliyar ruwa, isa da sakwannin yin rigakafi cikin lokaci da kuma aiwatar da ayyukan daukar matakan gaggawa.

Shugaban Sin ya kuma jaddada wajabcin tabbatar da tsaro muhimman shingayen tare ruwa kan muhimman tafkuna da kuma manya da matsakaitan wuraren tsimin ruwa, da kuma muhimman gine-gine.

Mista Xi ya kuma ba da umunin kara yin kokari domin tabbatar da tsaron jama'a, musamman ma sake tsugunar da mutane zuwa yankuna masu kariya, musamman tsofaffi da kananan yara da iyayensu 'yan ci rani suka bari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China