in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tayi tur da kaddamar da hari kan dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika a Somaliya
2016-06-11 13:20:03 cri
Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon yayi Allah wadai da kaddamar da hari kan dakarun kasar Habasha dake aiki a tawagar wanzar da zaman lafiya ta Afrika AMISOM a sansaninta dake Halgan a kasar Somaliya, sannan ya jaddada bukatar ga kasashen Afrika dasu jajurce wajen yakar kungiyar Al Shabaab da masu tsattsauran ra'ayin addini.

Ban ya bayyana goyan baya da kuma yawaba kokarin AMISOM da dakarun sojin kasar Somali wajen kwarewarsu da kuma jarumtar da suke nunawa wajen murkushe masu kaddamar da hare hare a kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar Somaliya.

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamar da harin, kuma tace ta hallaka a kalla sojojin kasar Habasha 60 a sansanin sojin.

Sai dai AMISOM ta musanta ikirarin da Al-Shabaab tayi, tana mai cewa dakarunta sun samu nasarar fatattakar maharan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China