Wani jami'in sojin Somaliya Ali Digaal shi ne ya tabbatar da hakan, a cewarsa an yi dauki ba dadin ne a a wani yanki kusa da garin Barowe dake shiyyar Shabelle.
Digaal ya shedawa 'yan jaridu cewar, fadan ya barke ne a lokacin da mayakan na Al-Shabaab suka yi yunkurin bude wuta kan tawagar mayakan wanzar da zaman lafiyar a kan hanyarsu ta zuwa garin Barowe.
To sai dai kungiyar ta Al-shabaab ta yi ikirarin cewa ita ce ta yi nasara, har ma ta ambata cewar ta kone 3 daga cikin tankokin yakin dakarun na AMISCOM.
Dakarun wanzar da zaman lafiyar dai, na ci gaba da farautar mayakan na Al-Shabaab a yankuna da dama na kudancin birnin Mogadishu. (Ahmad Fagam)