Bikin "Sa ido kan al'adun kasashen Afirka na shekarar 2016", wani muhimmin kashi ne na fannin al'adu dake cikin shirin ayyukan Johannesburg daga shekarar 2016 zuwa ta 2018 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bana ma'aikatar al'adu ta Sin za ta gayyaci kungiyoyin nuna fasahohi daga kasashen Afirka sama da 20 zuwa kasar Sin, domin nuna fasahohi da yin bikin nune nune sama da dari daya a larduna da birane sama da 10 na Sin. A matsayin wani muhimmin mataki na bikin "Sa ido kan al'adun kasashen Afirka na shekarar 2016", an kaddamar da bikin nune-nunen zane-zane mai taken "Alamar kasashen Afirka" a sa'i daya.(Fatima)