Domin kalubalantar barazanar ta'addanci a doron kasarta, Burkina Faso, kasa ta goma sha daya dake taimakawa MDD dake sojoji, na shirin janye rabin sojojinta dake yankin Darfour, a cewar ma'aikatar tsaron kasar.
Tare da bullowar kungiyoyin ta'addanci a kasar Mali, idan da gamayyar kasa da kasa ba ta tura sojoji ba domin kawo dauki ga shiyyar, da akwai yiyuwar cewa kungiyoyin ta'addanci dake dauke da makamai ba zasu tsaya a arewacin tafikin Nijar ba amma zasu wuce nan, in ji manjo janar na rundunar sojojin Burkina Faso, Pingrenoma Zagre.
Kasar Burkina Faso, kamar sauran kasashen shiyyar yammacin Afrika na fama da barazanar ta'addanci.
A tsakiyar watan Janairu, wani harin ta'addanci da kungiyar Al-Qaida reshen yankin Maghreb wato AQMI yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 30. (Maman Ada)