A daren ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2015 ne, aka sace tare da cin zarafin wasu mata a birnin Köln da ke kasar ta Jamus, lamarin da ya tayar da hankulan jama'a sosai a kasar Jamus.
Jamusawa sun shafe kwanaki a jere suna gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan wannan batu.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Jamus ta bayyana cewa, 'yan sandan kasar sun tabbatar da cewa, daga cikin mutanen da ake zarga da aikata laifin, har da 'yan gudun hijira fiye da 20 da wadanda suke neman mafaka. Ministan dokokin shari'a na kasar Jamus Heiko Maas ya jaddada a jiya cewa, ba za a iya tabbatar da cewa, ko dukkan 'yan gudun hijira suna bin dokoki ko a'a bisa wannan batu ba. Amma Maas ya yi nuni da cewa, batun cin zarafin mata a Köln batu ne da aka tsara shi, hukumomin shari'a na kasar Jamus suna gudanar da bincike don gano wadanda ke da hannu wajen tsara cin zarafin. (Zainab)