in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya ce babu hujja kwakkwara na rage darajar kudin kasar
2016-06-29 12:15:26 cri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kakkausar suka game da shawarar rage darajar kudin kasar Naira, ya ce, har yanzu bai gamsu cewa matakin zai warware matsalar tattalin arzikin kasar da kuma samar da makoma mai kyau ga kasar ba a nan gaba.

Buhari, ya bayyana rage darajar kudin kasar a matsayin marar hujja, cikin wani jawabi da ya gabatar a Abuja, shugaban ya ce, har yanzu babu wani gamsasshen bayani da ya samu daga babban bankin kasar game da tasirin da hakan zai yi ga ci gaban kasar.

Sai dai an yi amanna cewar, kasar ta karya darajar kudinta cikin wannan wata, ta hanyar shirin da babban bankin kasar ya bullo da shi na baiwa 'yan kasuwar musayar kudade wuka da nama wajen tafiyar da harkokin kasuwar.

Gwamnatin Najeriya ta sanar da sabon tsarin ne da nufin cike gibin faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya wanda ke matukar haifar da koma baya ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Tun bayan aiwatar da wannan sabon shiri, 'yan kasuwar na da ikon rage farashin sayen dalar Amurka.

Dama dai kwararru a fannin hada hadar kudade su bayyana cewar, nan gaba kadan komai zai daidaita game da kudin kasar, sai dai shugaba Buhari ya ce, rage darajar Nairar da aka yi a lokutan baya bai haifar da sakamako mai kyau ba ga kasar, sai ma ya kashe darajar kudin kasar ne kawai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China