in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abasanjo ya yi kira da a kafa kudi na bai daya a yammacin Afrika
2016-07-06 13:06:51 cri

Shigar da kudi na bai daya daga wajen kasashen yammacin Afrika zai bunkasa dunkulewa da ci gaban tattalin arzikin shiyyar, in ji tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo a ranar Litinin.

Tsohon shugaban ya yi wannan furuci a yayin wata ganawa tare da shugaban kwamitin gamayyar tattalin arzkin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, mista Marcel de Souza, a Abeoukuta, wani birnin dake kudu maso yammacin Najeriya.

Lokaci ya yi da kungiyar ECOWAS ta fara yin amfani da wani kudi na bai daya, in ji mista Obasanjo, ya kara da cewa, yin hakan zai taimakawa ci gaban tattalin arzikin dukkan kasashen shiyyar.

Wata dunkulewar tattalin arziki mafi zurfafa a cikin yankin ECOWAS za ta kawar sannu a hankali da yawan zaman kashe wandon matasa, in ji Obasanjon. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China