in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya zai aiwatar da kasafin kudin kasar na 2016
2016-07-19 10:59:51 cri

Fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa, shugaban kasar zai aiwatar da batutuwan dake kunshe cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara bi da bi.

Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya ba da tabbacin hakan a Abuja, a lokacin da ma'aikatu da hukumomin kasar suka gabatar da kasafin kudin su ga majalisar dokoki ta kasa.

A cewarsa, bisa abin da ke kunshe cikin kasafin kudi na babban bankin kasar CBN, da kamfanin mai na NNPC, da hukumar sufuri ta ruwa NPA suka gabatar, ya nuna a fili yadda shugaban kasar ke gudanar da gwamnatinsa ba tare da kunbiya kunbiya ba.

Shehu ya ce, gabatar da kasafin kudin da ma'aikatun gwamnati na kasar suka yi, musamman kamar su CBN da NNPC, abu ne da ba'a saba ganinsa ba a kasar.

Ya ce, shugaban kasar ya sha alwashin aiwatar da kasafin kudin kasar bisa doka, kana ya jaddada aniyar shugaban kasar wajen gudanar da gwamnati mai tsabta don samar da ci gaban kasa, da bunkasuwar tattalin arzikin kasar domin inganta rayuwar al'ummar Najeriyar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China