An ruwaito cewa, bangarorin biyu da suka gwabza fada da juna, sun hada da rundunar sojoji masu 'yantar da jama'a ta Sudan ta SPLA da ke karkashin jagorancin shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da kuma dakaru masu adawa da rundunar a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Riek Machar.
Da yammacin ranar 8 ga wata bisa agogon wurin, an ji amon musanyar wuta a wurin dake kusa da fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu, daga nan rikicin ya fantsama zuwa duk birnin na Juba. A wancan rana kuma, mutane fiye da 100 sun mutu sakamakon rikicin. Daga baya, kura ta lafa a ranar 9 ga wata, amma rikicin ya sake barkewa a ranar 10 ga wata.
Bisa labarin da kungiyar musamman ta MDD da ke kasar ta bayar a kan shafinta na sadarwa jiya, an ce, an tafka kazamin fada a wajen ginin MDD da ke bayan garin Juba.
Haka kuma kafar watsa labarai ta BBC ta ba da labarin kakakin Riek Machar da ya furta jiya cewar, sakamakon tsanantar rikicin a tsakanin bangarorin biyu, yakin basasa ya sake barkewa a kasar Sudan ta Kudu.(Kande Gao)