A jiya Talata da dare, Sinawa fiye da 70 sun tashi daga birnin Juba, hedkwatar kasar Sudan ta Kudu, inda ake fama da tashe-tashen hankali zuwa birnin Nairobi na kasar Kenya.
An ba da labari cewa, galibin Sinawa da suka isa birnin Nairobi su ne ma'aikatan kamfannonin Sin dake kasar Sudan ta kudu.
Ma ba da taimako ga babban wakilin kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu Wang Cun ya bayyana cewa, a jiya Talata, kura ta lafa a birnin Juba, lamarin da ya baiwa mutanen kasashen waje da dama barin kasar Sudan ta kudu.
Mr. Wang ya ce, bayan barkewar rikicin, ofishin jakadanci na kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu ya tuntubi kungiyar kasuwanci ta Sin da kamfannoni kasar Sin dake kasar, domin gabatar da shawara da kuma taimakawa ma'aikata Sinawa wajen tashi daga birnin Juba. Bisa taimakon da aka bayar, ofishin jakadancin Sin ya tabbatar da wurare 9 inda Sinawa za su taru don kwashe daga birnin Juba.(Lami)