Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi ya jaddada bukatar da ke akwai ta kare matasa daga shiga ayyukan ta'addanci da dakaru masu tsattsauran ra'ayi.
Liu wanda ya bayyana hakan yayin wata muhawara da aka shirya kan irin rawar da matasa za su taka wajen yaki da ta'addainci tare da samar da zaman lafiya, ya kuma bayyana ayyukan ta'addanci a matsayin manyan abokan adawar bil-adam.
Don haka ya ce, kamata ya yi al'ummomin kasa da kasa su dauki matakan da suka dace wajen yaki da duk wani nau'i na ta'addanci da ayyukan nuna tsattsauran ra'ayi. Sannan a samar da yanayi da ya dace na inganta ci gaban matasa a duniya. (Ibrahim)