Gungun G7 ya bayyana a ranar Litinin niyyarsa na kara rubunya kokari da nufin yaki da ta'addanci da hana samar da kudi ga 'yan ta'adda. Shugabannin kasashen Jamus, Canada, Amurka, Faransa, Italiya, Japan da kuma kasar Ingila sun yi wannan nuni a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a ranar Litinin bayan kammala tattaunawa ta yini biyu a Garmisch-Partenkirchen, birnin da ke kudancin kasar Jamus. Haka kuma sun tattauna batun ta'addanci tare da shugabannin gwamnatocin kasashen Afrika, da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa, a yayin wani zaman taron da aka fadada da taron G7.
Yaki da ta'addanci da hana samar da kudi ga 'yan ta'adda na daya daga cikin manyan batutuwan da taron G7 ya fi mai da hankali a kai.
Za mu ci gaba da mai da martani bisa daukar mataki yadda ya kamata, kuma za mu karfafa aikinmu cikin hadin gwiwa, in ji sanarwar. (Maman Ada)