in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kira da a hada karfi da karfe wajen yaki da tsattsauran ra'ayi
2015-04-23 10:43:10 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya ce, ya zama wajibi kasashen duniya su dunkule wuri guda, wajen aikin dakile yaduwar akidu na masu tsattsauran ra'ayi.

Mr. Ban wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labaru, bayan kammala zaman muhawarar MDDr, game da zakulo hanyoyin karfafa juriya, da yaki da ayyukan ta'addanci, ya ce, duk da cewa masu tsattsauran ra'ayi na alakanta kan su da wasu addinai, a hannu guda ayyukansu ba su da nasaba da koyarwar ko wane addini.

Ban ya kara da cewa, malaman addinai suna da rawar takawa, wajen aiwatar da sulhu, da magance rarrabuwar kawunan al'umma, tare kuma da yaki da masu munanan akidu.

Babban magatakardar MDDr ya kuma bayyana aniyar majalissar, na kaddamar da wani cikakken shirin kandagarki daga ayyukan ta'addanci, wanda za a kaddamar nan gaba cikin wannan shekara.

Taron na yini biyu wanda aka bude a ranar Talata, ya samu halartar wakilan gwamnatoci, da wakilan addinai, a gabar da kuma ake ci gaba da bayyana damuwa game da yaduwar ayyukan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kamar IS, da Boko Haram, da Al Shabaab. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China