Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame wanda ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a yayin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka karo na 27 da ya gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda, ya jaddada muhimmancin mayar da tsarin tattalin arzikin nahiyar zuwa na zamani domin cimma nasarar burin da aka sanya a gaba na farfado da nahiyar.
Shugaba Kagame ya kuma jaddada cewa, muddin ana bukatar cimma burukan da aka sanya a gaba a nahiyar, wajibi ne a hade manufofin inganta kasuwannin nahiyar da tsarin sadarwa na zamani ta yadda zai dace da bukatun al'ummomin kasashen, a kokarin da ake yi na samar da kasuwar bai daya ta kasashen nahiyar.
Bugu da kari, amfani da fasahar sadarwa ta zamani, wata kafa ce da za ta kara taimakawa wajen bunkasa kokarin nahiyar ta fuskar fasahar kirkire-kirkire wadda za ta taimaka wajen bunkasa jin dadin jama'a da tattalin arziki mai dorewa a Afirka.
Haka kuma wannan fasaha za ta saukakawa nahiyar samun bayanai da harkokin sadarwa a bangaren tattalin arziki. (Ibrahim)




