in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta nuna farin ciki game da farfadowar yanayin kasar Turkiyya
2016-07-18 20:18:45 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin na matukar farin ciki game da farfadowar yanayi a kasar Turkiyya.

Mr. Lu ya bayyana cewa, a halin yanzu, an farfado da yanayin kwanciyar hankali a kasar Turkiyya. Sin na matukar fari ciki da ganin haka. Ya kuma kara da cewa, kasar Turkiyya, muhimmiyar kasa ce a yankin gabas ta tsakiya, tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen shimfida zaman lafiya a wannan yanki. A daya bangaren kasar Sin ta goyi bayan kokarin da kasar Turkiyya ke yi wajen kiyaye tsaro da zaman lafiya a kasar.

A game da batun Gulen, Mr. Lu Kang ya bayyana cewa, ba shi da masaniya ta hakika kan sa. Ya nanata cewa, a matsayin kawa ta kasar Turkiyya, kasar Sin tana fatan kasar Turkiyya za ta iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali."(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China