in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU da Turkiyya sun cimma yarjejeniya domin magance kwararar 'yan ci rani
2015-11-30 10:40:18 cri

Kungiyar tarayyar Turai (EU) ta sanya hannu a ranar Lahadi kan wata yarjejeniya da kasar Turkiyya, game da ba da biliyan 3 na Euro kwatankwacin dalar Amurka biliyan 3.18 na taimako da kuma shigar kasar cikin gamayyar ta kasashe 28, tare da tunkarar da matsalar kwararar 'yan ci ranin da ba bisa doka ba.

Shugaban kwamitin tarayyar Turai Donald Tusk ne ya yi wannan sanarwa a yayin wani taron manema labarai bayan wannan taro na ranar Lahadi, wanda aka samu halartar shugabannin gamayyar kasashe 28 da kuma faraministan Turkiyya Ahmet Davutoglu dake ziyarar aiki a birnin Brussels.

Brussels na shawarwari tun cikin watan Satumba tare da Ankara domin karfafa sanya ido kan iyakarta da kasar Girka, bisa manufar magance kwararar 'yan ci-rani ko kuma 'yan gudun hijira a yayin da tarayyar Turai take fama da matsalar 'yan ci-rani mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu.

A cikin wannan shirin aiki da bangarorin biyu suka rattaba hannu, EU za ta baiwa Ankara biliyan 3 na Euro domin taimaka mata wajen kyautata hanyoyin zaman rayuwa na masu neman hijira a kasar Turkiyya. Biliyan 3 na Euro, an ba su ne ga 'yan gudun hijira na Syria, ba kasar Turkiyya ba, in ji mista Davutoglu.

Haka kuma EU ta amince da gaggauta ayyukan neman shigar Turkiyya cikin tarayyar Turai, tare da kuma sassauta matakan shigar 'yan Turkiyya cikin tarayyar Turai ba tare da takardar Visa ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China