in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 41 sun mutu a sakamakon harin ta'addanci da aka kai a birnin Istanbul
2016-06-29 20:41:53 cri

Ofishin gwamnan jihar Istanbul ta kasar Turkiyya ya ba da sanarwa a yau Laraba cewa, harin kunar bakin waken da aka kai jiya Talata da dare a filin saukar jiragen sama na Ataturk ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 41, a yayin da mutane 239 suka jikkata.

Sanarwar ta ce, an tabbatar asalin wasu 37 daga cikin mutane 41 da suka mutu, ciki har da 'yan kasashen Turkiyya da Saudiyya da Iran da Ukraine da sauransu.

Firaministan kasar Turkiyya Binali Yildirim ya bayyana a gun taron manema labaru da aka kira a yau Laraba da safe cewa a wurin da lamarin ya faru cewa, akwai alamun da ke nuna cewa, kungiyar IS ce ta kai wannan hari, amma har yanzu, ana ci gaba da bincike don gano 'yan ta'adda da suka kai harin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China