in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin yakin Rasha ya yi harbin kashedi domin kaucewa tafo mu gama da jirgin ruwan kamun kifi na Turkiya a tekun Aegean
2015-12-14 13:38:23 cri

Wani jirgin ruwan yaki na Rasha ya yi harbin kashedi a ranar Lahadi domin kaucewa tafo mu gama tare da wani jirgin kamun kifi na Turkiyya a tekun Aegean, in ji ma'aikatar tsaron Rasha.

Jirgin na Rasha, Smetlivy, da ya yada zango a kilomita 22 daga tsibirin Girka na Lemnos, a arewacin tekun Egee, ya gudanar da harbin kashedi domin kaucewa wani hadari tare da wani jirgin ruwan kamun kifin kasar Turkiyya, a cewar ma'aikatar tsaron.

Ma'aikatar ta isar da bacin rai ga jami'in kula da harkokin soja na ofishin jakadancin Turkiyya dake Moscow, kuma bangaren Rasha ya kira shi domin ya amsa tambayoyi game da abkuwar wannan lamari.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa, ta yi wa wannan jami'in Turkiyya kashedi game sakamakon da zai biyo bayan wadannan ayyuka na rashin tunani, tare da bayyana damuwarta game da sabbin ayyukan tsokana daga bangaren Turkiyya. Jami'in kula da harkokin sojan na Turkiyya ya yi alkawarin sanar da hukumomin Ankara matsayin Rasha game da wannan batu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China