Shugaban taron MDD na 70 Mogens Lykketoft, ya ba da sanarwa a jiya Asabar, inda ya yi Allah wadai da juyin mulkin da wasu sojojin kasar Turkiyya suka shirya.
Ban da haka kuma, shugaban kwamitin kungiyar EU Jean - Claude Juncker da shugaban kwamitin zartaswa na nahiyar Turai Donald Tusk da wakiliya mai kula da harkokin waje da tsaro ta kungiyar EU Frederica Mogherini sun ba da hadaddiyar sanarwa cewa, kasar Turkiyya muhimmiyar kawa ce ga kungiyar EU, kungiyar EU ta goyi bayan gwamnatin kasar da jama'a suka zaba. Kungiyar EU ta kuma yi kira ga kasar Turkiyya da ta farfado da tsarin kasar cikin gaggawa, kuma za ta ci gaba da zura ido kan yanayin kasar Turkiyyar tare da kasashe membobin kungiyar EU.
Wannan yunkurin juyin mulki ya kawo cikas ga huldar dake tsakanin kasar Turkiyya da Amurka. Gwamnatin Turkiyya ta zargi Fethullah Gulen, wani 'dan kasar Turkiyya dake gudun hijira a Amurka wajen kitsa wannan juyin mulki, ta kuma nemi gwamnatin kasar Amurka da ta tiso keyarsa zuwa gida. Dangane da lamarin, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya bayyana a jiya Asabar a birnin Luxembourg cewa, kasar Amurka za ta yi nazari kan wannan batu, amma ya kamata kasar Turkiyya ta shaida laifin Fethullah Gulen. Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya nanata a jiya cewa, kasarsa za ta nace ga goyon bayan gwamnatin kasar Turkiyya, tana fatan kasar Turkiyya za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da ita domin tinkarar kalubale tare.(Lami)