Da yake magana a yayin zaman taron kwamitin zartarwa na babban taron kungiyar tarayyar (AU) karo na 27, da ya gudana a Kigali, Dokta Carlos Lopes, sakatare zartarwa na kwamitin tattalin arzikin MDD game da Afrika, ya nuna cewa 'yan Afrika dake ketare sun tura a jimilce dalar Amurka miliyan 71 zuwa nahiyar a shekarar da ta gabata, kimanin kashi 4 cikin 100 na jimilar kudin kayayyakin da ake samarwa a nahiyar Afrika.
Watakila wannan adadi zai iya karuwa a tsawon shekaru masu zuwa. Dokta Lopes ya jaddada cewa mutum guda mai digirin jami'a cikin shida a Afrika yana barin kasarsa ta asali, lamarin dake nuna cewa 'yan Afirka dake kasashen waje sun kasance masu ilimi sosai.
Jami'in ya ce ana son kafa dokoki kan damammakin da ake da su, domin baiwa dukkan kasashe damar kulawa da 'yan gudun hijira cikin mutunci, in ji mista Lopes a ranar Laraba.
Ko da yake abin ya zama dole ga 'yan Afrika su kaura zuwa wasu nahiyoyi bisa dalilin rashin damammaki a cikin kasashensu na asili, maganar kaurar da mutane suke yi na kasancewa wata babbar matsalar kasa da kasa, dake bukatar duniya baki daya ta maida hankali a kai, in ji jami'in.
Wasu alkaluman da MDD ta tattara sun nuna cewa, kusan 'yan Afrika miliyan 250 suke rayuwa a yanzu haka a wajen kasashensu na asali. (Maman Ada)