Kwamandan sojojin ruwa na kasar Afrika ta Kudu Real Admiral Mhlana da karamin jakadan Sin da ke birnin Cape Town, da jami'an ofishin jakadancin Sin da ke kasar Afrika ta Kudu da na birnin Cape Town, da sauran hukumomin Sin da wakilan Sin da Sinawa dake kasar, da wasu sojojin kasar, gaba daya mutane fiye da 500 ne suka je tashar jiragen ruwa don tarbar ayarin jiragen ruwan yaki na Sin.
Yayin da suka ziyarar a kasar, jagoran ayarin janar Chen Qiangnan zai gana da kwamandan ayarin sojojin ruwa na kasar, da kwamandan sansanin sojojin ruwa na Simonstown da shugaban gundumar wurin. Ban da wannan kuma, ayarin zai halarci wasu bukukuwa, kana za su yi shawarwari da sojojin ruwa na kasar tare da halartar wata liyafa, da gasar wasan kwallon kafa ta sada zumunta. Bayan ziyarar, ayarin zai yi atisayen soji da sojojin kasar a tekun da ke kusa da wurin.(Bako)