Kasashen Afrika na fuskantar biyan karin kudin ruwa yayin da suka bi bashi a bana
A kwanan baya ne, mataimakin babban jami'i a asusun ba da lamuni na duniya IMF David Lipton ya ziyarci kasar Kenya, inda ya bayyana cewa, sakamakon gudanar da manufar tsuke bakin aljihu a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya, a bana, kasashen Afrika da suka ci bashi ciki har da Kenya, za su biya kudin ruwa mai yawa.
Bisa labarin da aka samu, an ce, a shekarar 2016, kasar Kenya ta yi shirin fidda takardun bashi da yawansu ya kai kudin Amurka miliyan 600 da kasashen Turai ke bin kasar bashi. (Bako)