Sirleaf, wanda kuma itace shugabar kungiyar samarwa mata sana'o'i a fannin noma wato EWA, ta furta hakan ne a lokacin da take ganawa da 'ya'yan kungiyar a lokacin gudanar da taron kolin kungiyar AU karo na 27 a Kigali na kasar Rwanda.
Kasar Rwanda, itace ke karbar bakuncin taron na wannan karo tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga wannan wata, mai taken shekarar 2016 ta 'yancin dan adam, tare da ba da fifiko ga hakkin mata.
Shugabar ta Laberiya tace, mata suna bada gagarumar gudumowa wajen cigaban aikin gona a Afrika, sai dai har yanzu suna fama da matsaloli iri iri, musamman na komadar tattalin arziki. Ta ce lokaci ya yi da za'a baiwa mata dama domin su bada tasu gudumowar wajen gina kasa.(Ahmad Fagam)