IMF ya ce, dalilin da ya sa tattalin arzikin Afrika ta Kudu ya samu koma baya har zuwa matsayi na uku shi ne raguwar darajar kudin kasar wato Rand.
Sai dai a ganin wani jami'i na sashen kula da hadari na reshen Afirka ta Kudu na kamfanin ba da shawara game da hada-hadar kudi na duniya KPMG, ya ce, har zuwa yanzu, tattalin arzikin Afrika ta Kudu shi ne mafi kyau a nahiyar Afirka, sabo da tsarinsa ya shafi fannoni da sana'o'i daban daban.(Bako)