Wannan haduwa za ta kasance wani tsari ga masana na kwamitin kwararrun kasuwanci da na kwastan wajen mai da hankali ga kafa wata kasuwar shiyya a tsakiyar Afrika, in ji kungiyar CEEAC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Wannan kasuwar da ake magana a kai za a kafa ta bisa tsawon shekaru goma, bisa wani shirin cigaba na 'yancin yin musanya, da ke kunshe da kafa wani yankin kasuwanci cikin 'yanci ta hanyar kawar da dukkan shingaye na kwastan, na hukuma da ma makamantansu dake da nasaba da kasuwanci a tsakanin kasashe mambobi. (Maman Ada)