in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 115 sun rasu sakamakon ricikin dake tsakanin bangarorin rundunar sojan Sudan ta Kudu
2016-07-10 13:31:48 cri
Bisa labarin da kungiyar adawa da rundunar sojojin jama'ar Sudan ta bayar a jiya Asabar, an ce, rikicin da ya tashi a daren ranar 8 ga wata tsakanin bangarori daban daban na rundunar sojan kasar a babban birnin kasar Sudan ta Kudu, Juba ya haddasa rasuwar mutane 115.

Kakakin kungiyar adawar William Gatjiath, ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, galibin mutanen da suka rasu sojoji ne, gawawwakinsu sun cika dakin ajiye gawawwaki na asibitin koyarwa dake Juba.

Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, kungiyar adawa da rundunar sojojin jama'ar kasar Sudan tana karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar.

Daga bisani kuma, Mr. Gatjiath ya ce, adadin mutanen da suka mutu a rundunar soja mai goyon bayan Machar ya kai kimanin 35, a yayin da mutane 80 ne suka rasu na rundunar sojan Sudan dake karkashin jagoranci shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir.

Da yammacin ranar 8 ga wata, an yi musayar wuta a wurin dake kusa da fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu, sa'an nan, rikice-rkice sun fara bazuwa a wurare daban daban dake birnin Juba, ya zuwa yanzu, ba a gano dalilin da ya haddasa tashin hankalin ba, amma Mr. Kiir da Mr. Machar sun kafa wani kwamitin musamman domin gudanar da bincike kan wannan lamari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China