in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Sudan ta Kudu sun dauki niyyar aiwatar da yarjejeniyar dangantakarsu
2016-06-06 09:56:44 cri

Sudan da Sudan ta Kudu sun jaddada a ranar Lahadi niyyarsu ta aiwatar da yarjejeniyar dangantaka da suka rattaba hannu tsakaninsu a shekarar 2012.

Kwamitin hadin gwiwa na siyasa da tsaro tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu ya yi wata ganawa a ranar Lahadi a birnin Khartoum tare da halartar ministocin harkokin waje, tsaro da man fetur na kasashen biyu. Ministan harkokin wajen kasar Sudan ta Kudu, Deng Alor ya bayyana cewa, abu mai muhimmanci shi ne, muna son warware dukkan matsaloli da kuma ci gaba da yin hadin gwiwa domin samun bunkasuwa tare. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China