Kasar Sudan ta Kudu ta soke a wannan shekara dukkan bukukuwan da aka tsai da shiryawa domin sallar samun 'yancin kai, bisa dalilin matsalolin tattalin arziki da kasar take fuskanta bayan shekaru biyu na yakin basasa da suka gurgunta bangaren man fetur din kasar.
Ministan watsa labarai, Michael Makuei, ya bayyana hakan a ranar Alhamis a cikin wata hira tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an dakatar da dukkan bukukuwan ranar 9 ga watan Yulin domin murnar samun 'yancin kan kasar, bisa dalilin matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta, tare da hauhawar farashin kayayyaki da kashi 300 cikin 100, bayan ja da bayan kudin Sudan Libre da kashi 90 cikin 100 a bisa hanyar faduwar darajarsa a shekarar 2015. (Maman Ada)