in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori 4 kan batun Gabas ta tsakiya sun yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su yi kokarin tabbatar da "shirin kasancewar kasashe biyu"
2016-07-02 13:53:56 cri

MDD da kungiyar EU da kasashen Amurka da Rasha wato bangarori 4 da batun Gabas ta tsakiya ya shafa sun ba da rahoto a jiya Jumma'a cewa, tarzomar dake faruwa da kuma yadda Isra'ila ke gina matsaugunan yahudawa suna kawo kalubale sosai ga aikin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, kana sun ba da shawara ga bangarorin biyu dasu farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya da kuma tabbatar da shirin kasancewar kasashe biyu.

Rahoton ya ce, bangarorin 4 sun nanata cewa, tabbatar da "shirin kasancewar kasashe biyu" ita ce hanya daya tak wajen tabbatar da dawamammen zaman lafiya, wanda zai iya biyan bukatun Isra'ila ta fannin tsaro, da cimma burin Palesdinu na kafa wata kasa mai zaman kanta, wanda har ila yau zai kawo karshen mamayewar da aka yi tun daga shekarar 1967 da kuma daidaita batun matsayin bangarorin biyu.

Bangarorin hudu sun ba da sanarwa game da wannan rahoto, inda suka yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su ba da hadin gwiwa wajen tabbatar da shawarwarin da aka gabatar cikin rahoton, domin share fagen farfado da shawarwarin daidaita batun matsayinsu.

A watan Yuli na shekarar 2013, Palesdinu da Isra'ila sun farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya da aka dakatar da shi har tsawon shekaru 3, amma sabo da rashin daidaito a tsakanin bangarorin biyu a kan batutuwan matsaugunan Yahudawa da sauransu, an dakatar da shawarwari daga watan Afrilu na shekarar 2014, kuma har zuwa yanzu, ba a farfado da shi ba tukuna. Tun daga tsakiyar watan Satumba na shekarar bara, yanayin tsaro ya kara tsananta a yankin Palesdinu da Isra'ila, inda ake shan fama da tashe tashen hankalin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China